Site icon Muryar 'Yanci

Shugabancin APC: Ba Tsige Ni Aka Yi Ba Wakilci Na Bayar – Mala Buni

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar rikicin da ya barke cikin jam’iyyar APC mai mulki ya dauki sabon salo yayinda wata wasikar Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ke karyata jawabin Gwamna Nasir El-Rufa’i.

Wasikar ta karyata jawabin El-Rufa’i na cewa Shugaba Buhari ya bada umurnin tunbuke Mai Mala Buni, a wata hira da gidan talabijin nawa Channel.

Hadiman Mai Mala sun bayyana cewa maigidansa ba korarsa aka yi ba, da kansa ya mika mulkin jamiyyar hannun Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, kafin tafiya jinya kasar Dubai.

Wani sashen wasikar mai dauke da kwanan watan 28 ga Febrairu tace: “Ina mai sanar da kai cewa zan tafi neman lafiya kasar UAE daga Yau, 28 ga Febrairu, 2022.”

“Saboda haka, na wakilta ayyukan ofishina na Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar nan gare ka.” “Ina kira ga mambobi su hada kai da Gwamna Abubakar Sani Bello ta hanyar bashi goyon baya kamar yadda kuka bani.”

Wani hadimin Buni, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa TheNation cewa: “Ba zai yiwu ace wani ko gungun gwamnoni sun cire Buni ba saboda wasikarsa a bayyana take.

Ya bi ka’ida kuma ya ce Bello ya wakilcesa.” “Gwamna El-Rufa’i ya fadawa Najeriya gaskiyar abinda ya auku tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni ranar Lahadi. Akwai kura-kurai cikin maganarsa.”

Exit mobile version