Site icon Muryar 'Yanci

Shugaban ‘Yan Sanda Ya Bada Umarnin Janye’Yan Sanda Masu Tsaron Manya

Babban Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan ‘yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan, ba tare da wani ?ata lokaci ba.

Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna, wadda ta ?auki kimanin makwanni biyu matasa na aiwatarwa.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin ‘yan sandan kasar nan a ranar Litinin kuma ya fara aiki nan take.

A bisa ga umarnin wanda ya fara aiki nan take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame kawai.

“Shugaban ‘yan sandan ya bada umarnin janye dukkan ‘yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai,”

“Duk wani kwamandan da ya saba wannan dokar zai fuskanci hukunci. Duk wani jami’in tsaro da aka kama yana tsaron wani babban mutum da makami ko babu, za a sauya masa wurin aiki kuma za a hukunta kwamandansa.”

An umarci dukkan ‘yan sanda masu tsaron da aka janye da su gaggauta zuwa gaban kwamandojinsu.

Exit mobile version