Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya taya Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III murnar cika shekara 15 kan gadon sarauta.
Shugaban ?asa Buhari a cikin sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin ya?a labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana Sarkin a matsayin mai gina zaman lafiya da jajircewa ga aikinsa, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata rayuwar alumma.
Buhari ya yi wa Sarkin Musulmi fatan samun wasu shekaru masu yawa kan matsayinsa tare da ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da ?abilu a sassan Najeriya.

