Mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu ba tare da ?ata wani lokaci ba, hakan na zuwa ne bayan an shafe tsawon lokaci ana kira ga shugaban da ya taimaka a bu?e kan iyakokin sakamakon halin u?uba da jama’a suka shiga dalilin rufewar.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa umarnin bude iyakokin zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020, wato ?arshen wannan shekara da muke ciki kenan.
Iyakokin guda hudu da za’a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nijeriya.
Sai kuma iyakar Seme da ke Jihar Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.
An ruwaito cewa ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin ganawarta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya
Sanarwar bude iyakokin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar NSMC ta kwatanta rashin tsaron Najeriya da rashin tsaron iyakoki, inda ta bayyana cewa hakan ne dalilin da yasa aka gaza cin nasara akan ‘yaki da ‘yan bindiga da Boko Haram.
?ungiyar ta ce matsawar gwamnatin tarayya tana son cin nasara a kan rashin tsaro ta wuraren tafkin Chadi, wajibi ne a kula kwarai da gaske. Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da za a tsare ‘yan Najeriya daga cutarwar ‘yan bindiga, kamar yadda mambobin kwamitin suka tattauna don samar da tsaro a kasar nan.

