Site icon Muryar 'Yanci

Shugaba Buhari Zai Ziyarci Kasar Amurka Yau Lahadi

Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Amurka ranar yau Lahadi domin halartar babban taron Majalisar ?inkin Duniya a birnin New York.

Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce a ranar Talata 14 ga watan Satumba aka bu?e taron karo na 76 wanda zai mayar da hankali kan farfadowa daga annobar korona da sake gini mai ?orewa da girmama ha??in ?an Adam da kuma yadda za a raya Majalisar ?inkin Duniya.

A ranar Juma’a shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a zauren majalisar, sannan zai ke?e da wasu shugabannin ?asashe da na hukumomin ci gaban ?asashen duniya.

Daga cikin tawagar shugaban da za su yi masa rakiya akwai ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da ministan shari’a Abubakar Malami da kuma karamin ministan muhalli Sharon Ikeazor.

Sanarwar ta ce sai a ranar Lahadi 26 ga watan Satumba ake sa ran shugaban zai dawo Najeriya

Exit mobile version