A ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Babatunde Raji Fashola, ya yi magana game da siyasar 2023 a gidan APC.
Babatunde Raji Fashola SAN ya ce yadda tsarin kama-kama ya yi aiki a zaben 2015, ya kamata idan an zo 2023, a bar mulki ya koma wa ya yankin kudu.
An ruwaito cewa Fashola ya yi wannan magana ne a lokacin da wasu ya yan APC suke kokarin ganin an bar ‘yan Arewa su cigaba da mulki.
Ministan da yake tattauna wa da yan jarida a Abuja, ya roki shugabannin jamiyyarsu su bi tsarin da aka dauko wajen zaben yankin da zai yi takara a 2015.
Fashola ya ce ya kamata a bi tsarin da ake tafiya a kai ko da ba a rubuta alkawarin a matsayin yarjejeniya ba, ya ce da an yi hakan, to da magana ta kare.
Amma ka da a karya alkawarin da yan uwa su ka yi, dole a cika alkawarin nan. Inji Fashola.
A cewar Raji Fashola, ya yan jamiyya za su iya cewa yanzu dan autan cikinsu ko mace ce za ta rike wata kujera, ya ce ko ba a rubuta ba, hakan ta zauna.
Mai magana da yawun jamiyyar APC mai mulki, Yekini Nabena ya shaida wa Punch cewa kafin zaben 2015, an tsara yadda za a yi takarar shugaban kasa.
Yekini Nabena yace shugabannin APC sun yarda a tsakaninsu cewa idan dan Arewa ya gama mulki, za a mika tikiti ne zuwa yankin kudancin Najeriya.
Da alamu rikicin da ake fama da shi a jamiyyar APC mai mulki shi ne inda za a kai tikiti a 2023.

