Site icon Muryar 'Yanci

Shari’a Sa?anin Hankali: Al?ali Ya ?aure Magatakardan Kotu

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Kaduna ta zartar da hukuncin daurin shekaru hudu a kan tsohon rijistaran kotun, Mista Joseph Etefia Udoh, bayan ya amsa laifin almundahana da kudin kotu N80m. Hukumar ICPC ce fara gurfanar da Mista Udoh da matarsa, ma’aikaciyar babbar kotun tarayya da ke Abuja, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja tun cikin watan Disamba na shekarar 2019 bisa tuhuma guda goma sha biyu.

Ana tuhumar Mista Udoh da matarsa mai suna Grace Udoh da gararumar kudi N80m da wani mutum da ake kara ya ajiye a kotun.

Mista Udoh ya zuba kudin a asusun matarsa tare da yin amfani da su wajen sayen manyan kadarori a manyan biranen Najeriya.

Udoh ya nemi sulhu, an rage yawan tuhumar da ake yi masa zuwa guda hudu yayin da aka ajiye dukkan tuhumar da ake yi wa matarsa. Bayan an karanta masa dukkan tuhumar da ake yi masa, Mista Udoh ya amince tare da amsa dukkan laifukansa.

Lauya mai gabatar da kara, Shehu Yahaya, ya roki kotun ta yankewa Mista Udoh hukunci bisa tanadin da doka ta samar na amincewa da sulhu kamar yadda ya ke a karkashin sashe na 270(10) na kundin hukuncin manyan laifuka na shekarar 2015. Da ya ke karanta hukuncin da kotu ta yanke, Jastis P. H. Mallong ya aika Mista Udoh zuwa gidan yari na tsawon shekara guda. Kazalika, kotun ta yanke hukuncin cewa ICPC za ta rike dukkan kadarorin da ta kwace daga hannun Mista Udo tare da yin gwanjonsu.

Exit mobile version