Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin ga watan Rabi’ul Awwal, shekara ta 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitra, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Nuwamba na shekarar 2020.
- Da alama mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta musu alkawarin hanya shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a, da za ta fito an jima da safe, don duba labarun da na kawo muku a wannan dandali nawa, daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis, a shafukana na jarida.
- Ana nan ana ci gaba da kiki-kaka tsakanin Gwamnatin Tarayya da malaman jami’a. Alamu na nuna Gwamnati na fama da matsin lamba, a kan lallai ta sasanta da malaman su koma aiki, su kuma malaman sun cije sai an biya musu dukkan bukatunsu. Sannan wata da watanni ba a biyan malaman albashi.
- Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 180 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 87
Oyo 51
Abuja 12
Filato 10
Edo 4
Ekiti 3
Ogun 3
Bauci 2
Kaduna 2
Neja 2
Kano 1
Ondo 1
Oshun 1
Ribas 1
Jimillar da suka harbu 63,508
Jimillar da suka warke 59,748
Jimillar da ke jinya 2,605
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,155
- Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku, da wasu sarakuna sun zanta da shugaban kasa Muhammadu Buhari, har ya tabbatar musu za a sanya kafar wando guda da ‘yan sanda baragurbi.
- Nan gaba kadan Gwamnatin Tarayya za ta soma tono man da ke yankin Tafkin Cadi.
- Kwamitin Majalisar Dattawa ya ce lallai ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsahirta da zuwa kasashen waje jinya ko neman magani, a tsaya a gyara asibitin gidan gwamnati. An ware wa asibitin Naira Biliyan 1.7 a kasafin gidan gwamnati na shekarar 2021.
- Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya, ya leka jihar Imo don ganewa idanunsa ofisoshin ‘yan sanda da aka kona kurmus.
- Soja daya ya riga mu gidan gaskiya, a fafatawar da sojojin suka yi da masu kai hare-hare a jihar Barno, inda sojojin suka kashe ashirin da biyar daga cikinsu
- Hukumar ‘Yan Bautar Kasa ta ce, tunda aka soma kwaronabairos a kasar nan, su ma sun yi sa’a irin ta jihar Kogi, babu dan bautar kasa ko ma’aikacin hukumar da ya taba harbuwa da kwarona.
- Ministar Kudi Zainab ta ce babu batun karin haraji, har da na Tamanin Kaya wato VAT.
- Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, ya je jihar Legas, jajanta wa gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu barnar da aka yi a jihar a lokacin zanga-zangar #ENDSARS.
- Donald Trump na zargin an tabka magudin zabe a wasu jihohi. Kotu ta ki amincewa da bukatarsa ta a dakatar da kidayar kuri’a, saboda alamun da ya gani zai kwashi kashinsa a hannun Joe Biden.
Mu wayi gari lafiya, mu yi Juma’a lafiya.
Af! Yau Juma’a mu dage da addu’a Allah Ya mana maganin duk wani abu da ke damunmu Amin.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=569632387172411&id=114506719351649
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

