Assalama alaikum barkanmu da asubahin Juma’tu babbar rana, goma sha uku ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Oktoba, shekarar 2020.
- Da yake ana cikin shagulgulan Maulidi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya shawarar su yi koyi da halayen Annabi Muhammad S.A.W. da ke cike da kauna, da yafiya, da fahimta. Ya yi wannan kira ne a sakonsa na Maulidi.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gaskiya tattalin arzikin Nijeriya ba zai iya sake jure wani sabon kulle na kwaronabairos ba, saboda haka ya ba ‘yan Nijeriya shawarar su ci gaba da kiyaye dokokin kauce wa yada cutar ko daukarta.
- Babban Bankin Nijeriya ya fitar da ka’idojin da za a bi wajen raba wa matasa naira biliyan 75 da gwamnati ta ware domin samar musu aikin yi.
- Saboda ci gaba da kamen wadanda suka yi wasoson kayan abinci da sauransu a sassa daban-daban na kasar nan, gidajen yari sun soma cika makil ana ta cunkoso ko cunkushe su da masu wasoson.
- Kwamishinan lafiya da sauran manyan mukarraban gwamnati bangaren lafiya musamman matakin farko a jihar Kogi, sun fashe da kuka da zubar da hawaye a lokacin da suka leka wajen ajiye magunguna suka tarar an wawushe komai. A jihar Adamawa kuwa an mayar da kashi 60 cikin dari na taraktocin da aka yi wasosonsu.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 150 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 89
Ribas 19
Ogun 11
Bayelsa 9
Kaduna 8
Filato 8
Taraba 3
Oshun 2
Delta 1
Jimillar da suka harbu 62,521
Jimillar da suka warke 58,249
Jimillar da ke jinya 3,131
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,141
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i da idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa za su cika shekara biyu suna zaman dakon ariyas na sabon albashi, sun soma korafin sun ji ana ta jin dilin-dilin a ko’ina tun daga shekaranjiya waccar, su kuwa har yau shiru kamar an shuka dusa.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, don karanta shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku a dandalina na soshiyal midiya, daga Juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Na lura kashi tamanin cikin dari da ke bibiyar rubutuna na kullum, ba sa iya tsayawa su karance rubutun daga farko zuwa karshe. Wasu sama-saman suke dubawa, wasu sukan kai tsakiya, wasu karshen kawai suke karantawa. Har wasu suka mun korafin rubutun yana yin tsawo da yawa. Misali Abba Zayyan tsohon shugaban gidan rediyon Nijeriya na Kaduna, ya ce mun shi can wajen da nake cewa AF kawai yake lekawa saboda duk labaran da zan kawo ya san su.
- An kuma tashi taro baram-baram tsakanin gwamatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i da ke nuna daliban jami’o’i na gwamnatin tarayya za su ci gaba da zaman gida, da wasu ke cewa ya taimaka wa wasoson da aka yi.
Mu wayi gari lafiya.
Af!
Allah ya yi wa Mal ABDULLAHI IDRIS (SHAWAI) rasuwa ranar Laraba 28-10-2020. Mai kimanin shekaru 65 a duniya, ya bar ‘y’aya da dama kuma ya shafe shekara sama da asin yana limanci a Guibi.
A garin Kudan kuma Allah Ya yi wa abokinmu Halidu Dankande rasuwa shekaranjiya da daddare, aka yi jana’izarsa jiya da safe. Yana aiki a jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Mun yi karatu a makarantar sakandare ta Kudan, kodayake suna ajin kasanmu.
Allah Ya jikansu, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.
SharhinIs’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

