Site icon Muryar 'Yanci

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, bakwai ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Oktoba na shekarar 2020.

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da wani taro da tsofaffin shugabanin kasar nan, su Yakubu Gowon, da Obasanjo, da Shonekan, da Babangida, da Abdulsalam Abubakar, da Jonathan a kan halin tsaro da kasar ke ciki. Buharin ya bayyana cewa a zanga-zangar #ENDSARS an kashe farar hula 51, da ‘yan sanda goma sha daya, da sojoji bakwai, aka kuma ji wa farar hula fiye da 37 rauni.
    Ya ce za a mayar da hankali ga samar da aiki ga matasa.
  2. Gwamnan jihar Zamfara Matawalle da na jihar Barno Zulum, sun roki a tura musu ‘yan sandan SARS jihohinsu domin su sun ga amfaninsu. Har Matawalen ya ce rashin ‘yan sandan na SARS ya sa ‘yan bindiga suka kashe fiye da mutum ashirin a Larabar da ta gabata a jihar tasa ta Zamfara.
  3. A jihar Kwara da Oshun, da Kuros Ribas jama’a na ta bi rumbunan da aka boye kayan tallafi na lokacin kullen kwaronabairos suna wawasonsu.
  4. Gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu ya shirya tsaf don gurfanar da wasu ‘yan sanda su 24 a gaban kuliya saboda zargin sun take hakkin jama’a.
  5. Zuwa yanzun mun tara naira tiriliyan goma sha daya da kusan rabi kudadenmu na fansho da muke adashinsu duk wata, a hannun hukumomin da ke tara su.
  6. Gwamnan jihar Legas ya yi gargadi da kashedi ga mutanen Legas da suka lalata dukiyoyin jihar da sunan zanga-zanga, cewa rashin hankalin ya isa haka nan.
  7. A yanzun wutar lantarki, da wuya ake samun ta sa’a hudu cikin sa’a ashirin da hudu. Yanzun haka rabonmu da wuta tun karfe goma na dare da suka dauke, har zuwa yanzun karfe hudu na asubah da nake wannan rubutu ba su kawo ba. Haka yinin jiya sai da almuru suka kawo ta. Ka fa biyan kudin wutar da ba a sha ba, ya samu gindin zama. Ga kudin na zama a duhu, duk yini naira dubu daya. Naira dubu talatin a wata.
  8. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  9. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Wasu malaman ma na jami’a wata da watanni ba albashi haka suke ta hakuri.

10 Ina ta lekawa dandalin da ake watandar alkaluman kwarobairos, ina tarar da ba a yi yankan alkaluman ba, tunda zanga-zangar #ENDSARS ta yi kamari kasuwar ta daina ci.

Mu wayi gari lafiya.

Af bature ya ce if you dont blow your trumpet you are waiting for someone to blow it for you, it will get rust. Ga wasu daga cikin mukaman da na rike :

RESPONSIBILITIES/POSITIONS:

I. TIMEKEEPER GOVT.DAY SEC.SCHOOL, KUDAN 1985 –
1986

II. ELECTORAL OFFICER A.B.U STUDENTS’ UNION 1991

III. SOCIAL DIRECTOR KUNGIYAR HABAKA HAUSA, A.B.U.ZARIA
1990-91

IV. ADVISER KAWO LADIES 1999 TO 2011

V. FIRST TRANSLATOR & HAUSA NEWSCASTER KADUNA STATE
TELEVISION 1996

VI. FIRST HAUSA TUTOR KADPOLY DEM.SEC.SCHOOL, 1997.

VII. FIRST HAUSA LECTURER SCHOOL OF PRELIMINARY & REMEDIAL
STUDIES, KADUNA POLYTECHNIC 2005.

VIII. PUBLIC RELATION OFFICER PARENT-TEACHER-ASSOCIATION
KADUNA POLYTECHNIC. 2000

IX. GRAND PATRON PRESS CLUB, KADUNA POLYTECHNIC DEM.SEC.
1998

X. SALES EXECUTIVE NATIONWIDE MANUFACTURING NIGERIA
LIMITED 1993.

XI. CHAIRMAN AND EDITOR-IN-CHIEF KPTDSS MAGAZINE JNR
SPIDER 2005 TO 2011.

XII. HEAD OF LANGUAGES DEPT. KAD POLY.DEMON.SEC.SCH. 2005
TO 2011

XIII. PRODUCER NEWS AND CURRENT AFFAIRS PROGRAMME
‘MADUBIN RAYUWA’ KSTV/CAPITAL TELEVISION 2004 TO 2013.

XIV. PRESENTER ‘HAUSA BA DABO BA’ KSTV/CAPITAL TV 2010 TO
2013.

XV. HOUSE MASTER (GREEN HOUSE) KPTDSS 2005 &2006

XVI. PATRON MAJALISAR ABOKAI MAI ZAMAN KANTA KASUWAR
BARCI, KADUNA. 2006 TO 2011.

XVII. SECRETARY PROTOCOL AND PUBLICITY SUB-COMMITTEE,
ASSOCIATION FOR PROMOTING QUALITY EDUCATION IN NIGERIA
(APQEN) 2006.

XVIII. CHAIRMAN PROTOCOL AND PUBLICITY COMMITTEE, 3RD SPEECH
AND PRIZE GIVING DAY, KADUNA POLYTECHNIC
DEMONSTRATION SEC.SCHOOL KADUNA. 2006.

XIX. ASSISTANT SECRETARY SABON GARI AL-NUR MULTIPURPOSE
CO-OPERATIVE SOCIETY, KADUNA 2006.

XX. CHAIRMAN PROTOCOL AND PUBLICITY COMMITTEE 4
TH
INTER-HOUSE SPORTS COMPETITION KADPOLY
DEMONSTRATION SEC.SCHOOL KADUNA 2007.

XXI. CHAIRMAN PROTOCOL AND PUBLICITY COMMITTEE 10
TH
ANNIVERSARY KADUNA POLYTECHNIC DEM.SEC.SCHOOL.
NOVEMBER 2007.

XXII. PATRON GREEN HOUSE KADPOLY DEMONSTRATION SECONDARY
SCHOOL. 2007.

XXIII. SECRETARY PROTOCOL AND PUBLICITY SUB-COMMITTEE
NATIONAL ASSOCIATION OF TEACHERS OF TECHNOLOGY. 2007.

XXIV.SECRETARY PROTOCOL AND PUBLICITY SUB-COMMITTEE
NATIONAL ASSOCIATION FOR PROMOTING QUALITY EDUCATION
IN NIGERIA 2006.

XXV. PATRON KINKINAU YOUTH PROGRESSIVE MOVEMENT
ASSOCIATION KADUNA. 2008.

XXVI.MEMBER ASSOCIATION OF TEXTILE TECHNOLOGY OF NIGERIA,

  1. (PUBLICITY AND INFORMATION COMMITTEE).

XXVII. HAUSA CONSULTANT/TRAINER, NEWAGE NETWORK 20O9 TO2010.

XXXVIII.CHIEF JUDGE ‘ZAKARAN GWAJIN DAFI’ A MUSICAL CONCERT
BY KARAMA RADIO & WISDOM PROMOTION PROJECT 8 – 10
th
OCTOBER 2011.

XXXIX. HAUSA CONSULTANT/TRAINER, NIGERIAN TELEVISION
AUTHORITY KADUNA CENTRE. 20 & 21 DECEMBER 2011.

XL. SENIOR MASTER ACADEMICS KADUNA POLYTECHNIC
DEMONSTRATION SECONDARY SCHOOL, KADUNA 2012.

XXXXI. PRODUCER/PRESENTER ‘HAUSA BA DABO BA’ ON KADA FM,
KADUNA STATE MEDIA CORPORATION. JANUARY 2012

XXXXII. HAUSA CONSULTANT/TRAINER, LIBERTY RADIO F.M.,KADUNA.
1 AND 2 JUNE, 2012.

XXXXIII. HAUSA GUEST ON FILIN MAKADA DA MAWAKA, ALHERI RADIO
DITV, KADUNA. 2012.

XXXXIIII. HAUSA CONSULTANT/TRAINER, RADIO NIGERIA, KADUNA.
25 & 26 JULY, 2012.

XXXXV. HAUSA CONSULTANT/TRAINER, KADUNA STATE MEDIA
CORPORATION (RADIO), 11 & 12 SEPTEMBER, 2012.

XXXXVI. MANAGING DIRECTOR/CHIEF EXECUTIVE, GUIBI-HAUSA
SERVICES, KADUNA. (REGISTERED WITH CORPORATE AFFAIRS) 2009 TO
DATE.

XXXXVII. TRANSLATOR OF THE TEMPLATE OF THE CONSTITUTION
REVIEW CONFERENCE OF KADUNA SOUTH ON SATURDAY 10
TH
NOVEMBER, 2012.

XXXXVIII. PRODUCER / PRESENTER ‘ADABIN HAUSA’ DITV ALHERI
RADIO KADUNA. JANUARY, 2013 TO 2014.

XXXXIX. MANAGER OF PROGRAMMES, SPIDER F.M. RADIO, KADUNA
POLYTECHNIC, KADUNA, MARCH, 2019 TO 2020.

Sai, ADHOC ASSIGNMENT BY BBC HAUSA, 2020.

Resource person, Freedom Radio, Nagarta Radio, KASU FM AND KADUNA MEDIA ACADEMY.

Member Pragmaric Association of Nigeria 2020.

Member Laboratory Committee, Languages Department, Kaduna Polytechnic 2019.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version