Site icon Muryar 'Yanci

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, ashirin da uku ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

  1. Ina ta lekawa Cibiyar Da Ke Aikin Dakile Cututtuka ta Kasa NCDC a takaice har zuwa asubahin nan ban ga ta fitar da sabbin alkaluman wadanda suka harbu da cutar kwaronabairos ba. Ko kudin da ke hannunsu ya kare ne sai an kuma hankada musu wasu?
  2. Mayakan Sama sun far ma wasu barayin shanu da ke kokarin satar shanun a yankin Kuzo da ke jihar A Kaduna, sojojin suka kashe da dama daga cikinsu.
  3. A yau litinin sauran ‘yan makaranta da ba su koma makaranta ba a jihar Kaduna, za su koma.
  4. A yau ake mika wa Sarkin Zazzau na goma sha tara, Ahmad Bamalli Sandar Girma.
  5. Sakamakon wata sasantawa tsakanin Gwamna Matawalle na jihar Zamfara da wasu kidinafas, kidininafas din sun sako wasu mata ashirin da shida, da suka yi kidinafin dinsu a yankin Faskari ta jihar Katsina.
  6. Ana nan ana ci gaba da tirka-tirka tsakanin Gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’i, dalibai na ci gaba da zaman kashe wando a gida. Sai dai daliban da ke jami’o’i na kudi wato masu zaman kansu, na ta karatunsu.
  7. Wata kungiya na ta fitar da fostar yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasa..
  8. Daidai lokacin da malaman jami’a ke kwashe wata da watanni ba albashi, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  9. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Daliban jami’o’i na Gwamnatin Tarayya ke gida suna zaman kashe wando. Daliban jami’o’i da ke zaman kansu/Jami’o’i na kudi, na makaranta suna ta karatu. ‘Ya’yan su waye ko su wane ne ke gida suna zaman kashe wando? ‘Ya’yan su waye ko su wane ne ke makaranta suna ta karatu?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version