Rahoton dake shigo mana daga birnin Daura na Jihar Katsina na bayyana cewar tsohon Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya mi?a takardar da ya cike da ke ?unshe da bayanan kadarorin da ya mallaka ga hukumar ?a’ar ma’aikata CCB bisa tanadin shafi na shida na Kundin tsarin mulkin ?asa.
Mai magana da yawun tsohon Shugaban, Garba Shehu cikin sa?on da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce a yau ne hukumar ta CCB ta tabbatar da kar?ar fom din tsohon shugaban ?asar.
A cewarsa, takardar bayanan ta nuna cewa kadarorinsa da za a iya sauyawa wuri ba su ?aru ba – a gida da kuma wajen Najeriya.
Sannan bai bu?e wani sabon asusun banki ba, baya ga wanda yake da shi a bankin Union a Kaduna.
Garba Shehu ya ?ara da cewa, tsohon Shugaban bai kar?i bashi ba kuma adadin shanunsa sun ragu saboda ya bayar da wasu kyauta cikin shekara hu?u da ta gabata.

