Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed tayi karin haske game da sababbin kudi da za a buga.
A wani bayani da aka fitar a shafin LinkedIn a ranar Alhamis, an fahimci ba haka nan za a kyale mutane su rika maida kudin hannunsu cikin bankuna ba, ba tare da sa ido ba musanman daga Hukumar EFCC.
Ministar tace za a hukunta duk bankin da ya sabawa kaidojojin da aka gindaya, Ministar ta bayyana cewar jamian hukumar EFCC da babban bankin Najeriya za su ri?a lura da duk kudin da suke shiga asusun jamaa.
Zainab Shamsuna Ahmed ta ?ara da cewa daga yanzu babban bankin Najeriya watau CBN zai rage adadin takardun kudin da yake bugawa lokaci zuwa lokaci.
A farkon shekarar 2023 ake tsammanin Gwamnan babban Banki CBN zai fitar da sababbin tsare-tsare da za a bi wajen ganin jamaa sun rage yawo da kudi a hannunsu.

