Shugaban ?asa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ?an Najeriya cewa nan bada jimawa ba abubuwa za su fara sauyawa zuwa farin ciki a Najeriya. Shugaban ?asar ya ba da wannan tabbaci ne yayin da ?an Najeriya ke fama da wahalhalun tsadar rayuwa sakamakon wasu sauye-sauyen gwamnati, The Cable ta rahoto.
Bola Tinubu ya ce yana sane da cewa yan Najeriya na korafi kan yunwa, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta fito da kayan jin kai domin a magance illolin yunwa.
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi, Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a fadar shugaban ?asa da ke Abuja, yayin bikin kaddamar da shirin mata na Najeriya.
Ya ce: “Gwamnatina zata tafi da mata kuma wannan na ?aya daga cikin tsare-tsare na, ina alfaharin tsayawa a gabanku yau kuma na gaya muku cewa goben matan Najeriya za ta yi kyau. “A matsayinmu na gwamnati aikinmu ne mu ba da fifiko ga yan ?asa masu rauni wa?anda sune mata da kananan yara.”
Da yake tsokaci kan halin yunwa da ake ciki, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa ta hanyar samar da tallafi domin al’umma su ci su ?oshi.
A yau ana nuna damuwa kan yunwa, zamu fito da kayan abinci domin kawar da duk wata illa ta yunwa, abubuwa sun yi wahala amma ba zamu zauna dindindin a haka ba. “Nan bada da?ewa ba abubuwa za su fara canzawa saboda zamu fito da ?arin abinci ga al’umma, sannan a shirye muke mu aiwatar da sabon mafi ?arancin albashi.”

