Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce ?asar Saudiyya ta kasance mai kyautatawa Najeriya, tsawon lokaci a tarihi.
Shugaban ya fa?i haka ne lokacin da yake ganawa da ministan harakokin wajen Saudiyya a ranar Talata a Abuja, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a cikin wata sanarwa.
Shugaba Buhari a cewar sanarwar ya shaida wa Yariman Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud cewa Najeriya mai dimbin jama’a kuma rauni ga abubuwan more rayuwa, kasar na dogaro ne da arzikin fetur domin samun ku?a?en shiga.
“Kuma Saudiyya ta kyautata muna, ta hanyar sadaukarwar rage man da ke samarwa saboda mu a lokuta da dama,” in ji shugaban.
Shugaba Buhari ya kuma ce dangantakar da ke tsakanin ?asashen biyu mai ?arfi ce.”
A nasa ?angaren a cewar sanarwar, Yarima Al-Saud ya mi?a sa?on gaisuwar Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud ga Buhari, yana mai cewa “Saudiyya ta yaba da ala?arta da Najeriya ta tsawon shekara 61 kuma tana fatan ?arfafa ta.”

