Gamayyar Kungiyoyin arewacin Nijeriya, ta fara gudanar da Zanga-zanga lumana, domin ganin jami’an tsaro sun kubutar da yara sama da dari ukku da talatin da ukku, daliban makarantar sakandire ta Kankara da ke hannun su, yau kusan kwana shidda.
Masu Zanga-zanga dauke da kwalaye dauke da rubutu a kwalaye daban daban, Kamar Bring “Back Our Boys” suna tafiya suna rera wakokin a sako wadannan dalibai da ke hannun yan bindiga.
Jagoran masu Zanga-zanga, Balarabe Rufa’i ya bayyanawa manema labarai cewa ” mun zo jihar Katsina ne, domin mu kara tunatar da gwamnatin tarayya cewa kokarin da suke bai Isa ba, kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba mu kunya, saboda halin-ko-in-kula da ya nuna kan sace wadannan dalibai.
Zanga zangar dai ba ta yiwu ba, saboda yanayin tsaro da jihar Katsina ke ciki, inda aka shawarce masu Zanga-zanga su bada korafin su a rubuce, kuma yau za’a damka wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari hannu da hannu, kuma suka aminta. Inda suka damka takardar hannun, mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara kan harkokin tsaro, Malam Ibrahim Katsina.

