Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar, sakamakon yadda matsalar tsaro ta satar Dalibai ke cigaba da ?amari a fadin Jihar.
Shugabar sashin kula da ingancin kayayyaki na ma’aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.
An aike da sanarwar ga shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun. Ta kuma yi gargadin hukuncin da ka iya biyo baya idan ba a bi umurnin ba.
Wani sashi na sanarwar ya ce: “Ana shawartar cewa a bi dukkan umurnin da ke cikin wannan wasikar domin akwai hukunci da zai biyo baya ga makarantun da ba su bi umurnin ba.”
Umma Ahmed ta ce matakin ya zama dole ne bayan sace dalibai da aka yi daga Bethel Baptist High School a Damishi da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Fiye da dalibai 100 ne aka nema aka rasa bayan harin da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a safiyar ranar Litinin. Sai dai rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce an ceto dalibai 26 cikin wadanda aka sace.
Sanarwar ta ce: “Bayan rahoton da hukuma ta samu game da barzanar tsaro a Bethel Baptist High School a Damishi, an yi taro da kungiyar masu makarantu masu zaman kansu (NAPPS) da wasu masu ruwa da tsaki a ranar Litinin 5 ga watan Yulin 2021 inda aka yanke hukuncin rufe wadannan makarantun daga ranar Litinin 5 ga watan Yulin 2021.”
Makarantun da abin ya shafa sune Faith Academy da ke Kachia Road da ke kallon Jakaranda; Deeper Life Academy, Maraban Rido; Ecwa Secondary school, Ungwar Maje, Bethel Baptist High School, Damishi, da St. Peters Minor Seminary, Katari. Saura su hada da Prelude Secondary School, Kujama; Ibiso Secondary School, Tashar lche; Tulip International (Boys) School; Tulip international (Girls) School; Goodnews Secondary School; St Augustine, Kujame; Comprehensive Development institution (CDI), Tudun Mare da Adventist College, Kujama.

