Jamiyyar PDP , tana goyon bayan kiraye kirayen da mutanan Katsina , wajen kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari, a matsayinsa na shugaban rundunar tsaron kasa, wanda yayi alkawarin jagorantar samar da gyara, da ya tabbatar an kwato daliban da aka sace awanni kadan bayan saukarsa dashi da rundunarsa ta tsaro a jihar.
Jamiyyarmu tace abun kunya a lokacin da ya kamata mutanan Katsina su samu nutsuwa saboda zuwan sa jihar,amma sai gashi abun ya faru a gaban idonsa? a cikin jiharsa, inda ya tafi hutu.
Sanarwar data fito ta hannun sakataren yada labarai na jamiyyar PDP Kola Ologbondiyan ta ce” wannan abun ya tabbatar da gazawar shugaban kasa Buhari wajen samar da jami’an tsaron da zasu rakasa.
PDP bataji dadin kauracewa gayyatar da majalissa tayiwa shugban kasa Buhari don tattaunawa akan matsalar tsaro , sai gashi ya watsar da nauyin dake kansa da sunan daukar hutu wanda hakan ya karawa yan ta’adda, yan daba, masu garkuwa da mutane.
Wannan ya tabbatar shugaban kasa Buhari , a matsayinsa na shugaban rundunar tsaro , ya baxai iya kare kasar nan ba, shiyasa dukkan yan Najeriya suna kira da kawai ya,sauka.
Gazawar shugaban kasa akan matsalar ta tabbatar da kiran da yan majalissar PDP sukayi na a tsige shugaban kasa kawai.
Muna da tabbacin da shugaban kasa Buhari ya amince da kiran da mu da yan
Najeriya da kuma dukkan zauran majalissar kasar nan na canza fasalin hukumar tsaron kasar nan, daya amince da yanzu bama cikin wannan matsalar.
Tabbas, wannan satar daliban da ajayi a jihar shugaban kasa , a gabansa, ya tabbatar da alamar tambaya akan yakin da suke da yan ta’adda.
PDP tana kira ga shugaban kasa Buhari da ya gaggauta janye hutun da yake a Daura ya fita neman wadannan daliban, tunda samar da tsaro yana wuyansa.
Muna kara mika jajanmu ga mutanan Katsina, musamman iyayan yaran da aka sace musu yaya, wanda suka dandana radadin rashin kwarewar gwabnatin Buhari.
PDP , zamu cigaba da aiki da sauran yan Najeriya wajen ganin ahugaban kasa Buhari ya samu wadannan daliban.
PDP tana kira ga yan Najeriya damu cigaba da addu a akan mugun yanayin da muke ciki, da jarabtar da muke ciki na rashin kwarewar gwabnati.

