Kakakin rundunar ?an sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya sanar da hatsarin mota da sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi a cikin garin Kano.
Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa Daya daga cikin motocin dake tare da Sarki Aminu ne ya gogi wata mota kirar Toyota a Gadar Lado. Nan take ya garzaya da direban motan zuwa asibitin Murtala domin a duba shi.
Rundunar yan sandan Kano ta karyata labaran da ake yadawa wai an kai wa sarki Aminu hari don a kashe shi ne.

