Fatima Isa Muhammad wadda aka fi Sani da Teemah Makamashi a harkar fim ta Masanaantar fina-finan Hausa ta Kanywood.
Ta na daya daga cikin manyan Jarumai da za a iya cewa ta wuce sahun yaran Jarumai duk da dai ba ta Kai sahun tsofaffi ba.
Ta dauki lokaci a cikin harkar don haka jaridar Dimukaradiyya ta zanta da ita Kan rayuwar ta a Masanaantar kannywwod.
Fatima Isa Muhammad ta ce To Alhamdulillahi, Ni harkar fim babu abun da zan ce, domin na samu rufin asiri a cikin ta, don haka sai godiya ga Allah.
Teemah Makamashi ta bayyana Babban abun da na fi alfahari da shi a cikin harkar fim, shi ne yadda na ke zama da kowa lafiya, domin ni daman a rayuwa ta ba na son fada da kowa, to kuma sai ya zama muna zama da kowa lafiya a cikin harkar, don haka wannan abin alfahari ne a gare ni.
A karse Teema ta yi kira ga abokan sanaar ta da su rinka mutunta juna da Kuma rike sirrin sanaar su.

