An bayyana cewar sai dukkanin ‘yan kasa sun bayar da tasu gudummuwa wajen samar da tsaro a ?asa kafin abubuwa za su tafi yadda ake bukata.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Liberty ya yi dashi cikin shirin Bakonmu na mako a karshen Mako.
Masari ya ?ara da cewar gudummuwar ‘yan ?asa ta fuskar tsaro ta zama wajibi ta la’akari da adadin yawan jama’a da Najeriya ke dashi, da kuma karancin jami’an tsaro, saboda haka idan aka kwatanta yawan jami’an tsaro da yawan jama’ar ?asa to a bayyane yake cewar aikin samar da tsaro ya fi karfin jami’an tsaro su kadai, aikine da ke kan kowane mahaluki a kasa.
Gwamnan ya bada misali da matakan da gwamnatin shi ke dauka a Jihar Katsina, inda ya bayyana cewar a kowace karamar hukuma da ?auyuka sun samar da kwamiti na jama’a wa?anda za su sanya ido akan tsaro, wannan kwamiti ya kunshi ‘yan sa kai da Matasa da dagatai da Ar?o Ar?o da masu unguwanni, har da shugabannin Mata, wa?anda za su sanya ido da bada gudummuwa wajen samun tsaro a Jihar.
Masari ya kuma bayyana yadda Gwamnatinshi ta mayar da hankali wajen gyaran hanyoyi a fadin jihar wa?anda za su taimakawa jami’an tsaro da sauran al’umma da?ile dukkanin wani farmaki daga ‘yan ta’adda.
Daga ?arshe Gwamnan ya shawarci ‘yan Najeriya gaba daya da su sanya kishin ?asa cikin al’amurran su, su ?auki damuwar Najeriya a matsayin damuwarsu ba wai damuwar wani bangare ba.
“Mu kalli matsalar a matsayin tamu ce gaba ?aya ba maganar Arewa ko kudu ba, idan muka sanya wannan kishin a zukatan mu babu shakka Allah zai taimaka mana wajen samun mafita”.

