Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya yi kira ga yan Najeriya kada su bar gwamnatin tarayya ka?ai wajen ya?i da matsalar tsaro, samar da tsaro nauyi ne dake akan kowa.
Da yake jawabi a Iyin-Ekiti, jihar Ekiti, Lawan ya bukaci yan Najeriya su ?auki matsalar da muhimmanci kuma su ?auka kowa na da rawar da zai iya takawa wajen shawo kan matsalar.
A cewar Kamfanin dillancin labarai, NAN, Sanata Lawan ya ziyarci Iyin-Ekiti ne bisa sarautar da basaraken Iyin-Ekiti, Adeniyi Ajakaye, ya ba shi.
“Shugabannin mu da suka kafa Najeriya sun fito daga yankuna daban-daban kuma daga addinai daban-daban, amma suna da manufa ?aya ta cigaban Najeriya.” “Sun fuskanci ?alubale sosai, amma sun magance su.
Yanzun wasu shugabanni sun zo da kudirin gyara ?asa da kawo cigaba. Yanzun muna fama da wasu matsalolin kamar na shugabannin baya.” “Yanzun matsalar tsaro ce tafi damun mu a fa?in kasar nan.
Wajibi yan siyasa, shugabannin addinai da kuma sarakunan gargajiya su ha?a kansu wuri ?aya.” Domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro.
Sanata lawan ya kara da cewa ko a wane yanki wa?annan matsalolin suke ya kamata mu ha?a karfi da karfe wajen magance su. “Bai kamata a bar gwamnati ka?ai ta dakile matsalar ba, abu ne na gaggawa, ya kamata mu ha?a kanmu wuri ?aya mu kawo karshen matsalolin da suka dame mu domin cigaban ?asa.”

