?an Majalisa mai wakiltar ?aramar Hukumar Charanchi a majalisar dokokin Jihar Katsina Honorabul Lawal Isah Kuraye, ya bayyana cewar yana da matu?ar muhimmanci jama’a su gane cewar aikin samar da tsaro a ?asa ba aikin gwamnati bane ita kadai, aikine wanda ya rataya a wuyan jama’a kowa da kowa.
Lawal Kuraye ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan bikin ranar dimukura?iyya a Kaduna.
?an majalisar ya kara da cewar an baro shiri tun rani ne sakamakon yadda aka yi watsi da Sarakunan gargajiya akan harkar tsaro aka koma rayuwa kara zube, wanda hakan ya bada gudunmawa wajen lalata tsaro a ?asa.
Kuraye ya tabbatar da cewar Sarakuna sune suke da sani da masaniya akan kowa dake yankin su, babu mai shiga ko mai fita face da sanin su, amma a yanzu duk an manta hakan dole muga ba daidai ba.
Dangane da bikin ranar dimukura?iyya da ke gudana kuwa Lawal Kuraye yace a magana ta gaskiya Shugaban ?asa Buhari ya yi rawar gani a sha’anin shugabanci idan aka kwatanta da baya, sai dai wasu matsalolin da ba a rasa ba wa?anda ke damun duniya baki ?aya.
Hakazalika ?an Majalisar ya kuma yaba gami da jinjina ga Gwamnan jihar Katsina Aminu Masar wanda ya bayyana shi a matsayin maceci wanda burin shi shine yadda zai ceto Jihar Katsina daga matsalolin da gwamnatocin baya na PDP suka tsunduma ta ciki.

