Site icon Muryar 'Yanci

Sai Mun Sauya Salo Za Mu Yi Nasara A Yaki Da Ta’addanci – Deby

Shugaban ?asar Chadi, Idris Deby Itno, ya bayyana ?warin gwiwarsa cewa dakarun ha?in gwiwa na ?asashe hu?u da ke ya?i da Boko Haram (MNJTF) za su kawo ?arshen ?ungiyar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar jim ka?an bayan ya gana da Shugaban ?asa Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban mai mu?amin soja na Marshal ya ce sababbin salon ya?i da rundunar ke ?auka, ciki har da sake shugabanninta a kowane mataki, za su taimaka wajen da?ile ayyukan masu i?irarin jihadi.

“Ganin sabbin matakan tsaro da ake ?auka da sabbin shugabannin tsaron, ba a Najeriya ka?ai ba har a rundunar Multinational Joint Task Force wadda ita ma ta yi sababbin kwamandoji, za mu iya kawo ?arshen ayyukan Boko Haram baki ?aya,” in ji shi.

“Abin ba?in ciki shi ne, dagewar da Boko Haram da IS ke yi a yankin Tafkin Chadi na da yawa sosai. Ana ba su horo da makamai daga Libya.

“MNJTF ta samu gagarumin ci gaba a ‘yan kwanakin nan. Samuwar sabon shugaban rundunar MNJTF za ta taimaka mana kawo ?arshen Boko Haram.”

Sojojin Chadi na da ?warewa sosai a ya?i da masu i?irarin jihadi a tsakanin ?asashen Najeriya da Nijar da Benin da Kamaru, wa?anda ke cikin rundunar ta ?asa da ?asa.

Exit mobile version