Site icon Muryar 'Yanci

Sai An Hada ?arfi Za A Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa a kasar da su ajiye batutuwan zabe a gefe guda kuma su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na magance matsalar tsaro a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da wasu jami’an jam’iyun suke shan ruwa a Fadar Aso Rock tare da wasu manyan ‘yan kasuwar kasar, inda ya ce rashin tsaro shi ne babbar matsalar da ke damun kowane dan Najeriya.

Shugaban ya ce a makon jiya, yayin taron babban kwamitin gudanarwa na jam’iyyarsa ta APC, an fitar da kwakkwarar matsaya cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kokarin karfafa turakun dimokradiyya a dukkan matakan mulki na kasar.

Exit mobile version