Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin afuwa ga fursunoni 11 daga gidajen yarin jihar domin murnar sabuwar shekarar 2023.
Wannan na ?unshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwaman kan kafofin ya?a labarai na gwamnan jihar Mista Muyiwa Adekeye ya fitar.
Afuwar ta shafi fursunonin da suka nuna kyakkyawan hali da wa?anda suke fama da rashin lafiya kamar yadda sanarawar ta bayyana.
Haka kuma gwamnan ya nemi al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya, tare da fatan cewa aikin da ya faro tun a shekarar 2015 domin inganta rayukan al’umma jihar za su ci gaba a gwamnati mai zuwa.

