Ruwan sama kamar da bakin kwarya da akayi yayi sanadiyar rugujewar gidaje sittin da shida da kuma lalata gonakai dari da hamsin a cikin karamar hukumar Shelleng dake jahar Adamawa.
Babban sakataren hukumar agajin gaggawa a jahar Adamawa ADSEMA Dr Muhammed Suleiman ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola.
Dr Muhammed Suleiman yace lamarin ya farune a kauyen Lababiri dake cikin gundumar Bàkta duk a cikin karamar hukumar ta Shelleng.
Dr Suleiman yace hukumar tasu da samu labarin aukuwar lamarin wanda kuma hakan yasa hukumar batayi da wasaba wajen kai dauki a wurin da ambaliyar ruwa yafaru.
Dangane da wadanda suka samu rauni ko akasin haka kuwa sai Dr Suleiman yace ya zuwa yanzu kam ba wani labari da suka samu dagane da haka saidai suna gudanar da bincike domin gano ko wana irin asara akayi sakamokon ambaliyar ruwan.
Babban sakataren yace wadanda lamarin ya shafa dai yanzu haka sun samu mafaka a makwabtan kauyen.

