Site icon Muryar 'Yanci

Rushe Makarantun Allo: Fa?a Ne Da Alkur’ani – Maraya

Sanannen Malamin Addinin Musulunci a Jihar Kaduna Sheikh Halliru Maraya ya yi martani dangane da matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin El Rufa’i ta ?auka na tarwatsa makarantun karatun Alkur’ani na Allo da sunan yaki da Corona a matsayin yaki ne kawai da makaranta Alkur’ani.

Sheikh Maraya ya bayyana hakan ne a yayin zantawar da gidan rediyon BBC Hausa ya yi dashi dangane da kaddamar da rusau da gwamnatin El Rufa’i ta fara yi akan makarantun Allo dake fa?in Jihar.

Malamin ya cigaba da cewar maganar da ake yi na cewar wai an dauki matakin yin hakan ne domin ya?i da Corona wannan ba gaskiya ba ne, domin idan cunkoso ake magana ai inda aka kai su yanzu ya fi zama hatsari a garesu na kamuwa da cutar.

“Hakazalika maganganun da wasu ke ya?awa da cewar wai inda makarantun allon suke basu da takardun izinin zama, wannan ma maganar banza ce, idan batun fili ne ai takarda ya kamata a li?a da rana ba wai azo cikin dare yara na barci a firgita su a kwashe su ba, saboda filin ne bai da izinin zama ba yaran ba”

Akwai wani kulli a zuciyar gwamnan akan Almajirai, domin idan cunkoso ne me yasa ba a kwashe yaran makarantar ‘ya’yan sojoji na NDA ba.

Exit mobile version