Site icon Muryar 'Yanci

Rundunar Soji Ta Na?a Sabon Kakaki

Rundunar Sojojin Nijeriya ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama’a na rundunar wato Kakaki.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Ana sa ran Yerima zai fara aiki a ranar Laraba 10 ga watan Fabrairun shekarar 2021, kamar yadda aka sanar cikin sanarwar.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Ya shiga aikin soja ne a Oktoban 1989 sannan daga bisani ya shiga sashin hulda da jama’a na rundunar. Yerima, wanda ke da digiri na fanin kimiyyar siyasa daga jam’iar Ahmadu Bello da ke Zaria ya yi aiki a wurare daban daban a rundunar soji.

Ya rike mukamin kakakin rundunar soji daga 1995 zuwa 1996; Kakakin makarantar horas da jami’an sojoji, NDA, daga 1996 zuwa 2000; kakakin soji a karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sierra Leone daga 2000 zuwa 2002; Mataimakin shugaban sashin watsa labarai daga 2007 zuwa 2009 da kuma direktan, sashin sadarwa na tsaro daga 2009 zuwa 2013.

Yerima mamba ne na Cibiyar Kwararrun Masu Hulda da Al’umma, NIPR, Masu Hulda da Al’umma na Afirka, APRA da kuma Kungiyar West Africa Society for Administration and Communication. Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban kwamitin sadarwa da watsa labarai na gaggawa, MICEM.

Exit mobile version