Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai rike masu ganin cewa gwamnatinsa ta gaza a cikin shekara biyar musamman a ?angaren tsaro a ransa ba.
Shugaban kasar ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabin sabuwar shekarar 2021 a ranar Jumaa.
Buhari ya ce yana sane akwai ?an Nijeriyar da basu gamsu da ?o?arin da gwamnatinsa ke yi ba tun ranar da ya zo kan mulkin kasar.
Saidai ya ce akwai bu?atar wadannan mutane su yi waiwaye daga lokacin da Buharin ya fara mulkin kasar da ci gaban da aka samu daga 2015 zuwa yau.
Shugaban kasar ya alakanta rikice-rikicen da ake samu a ?asar kan tsananin talauci, banbancin matsayi cikin alumma, da kuma sa?anin da ake samu tsakanin matasa.
Jawabin Shugaban ?asar dai na cigaba da ?aukar hankulan jama’a, musanman ta la’akari da yadda Shugaban ya ta?o abubuwa da dama da suka da?e suna ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.

