Mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich ya tabbatar da cewa zai sayar da kulob din.
Abramovich ya sanar da hakan ne a shafin intanet na Chelsea FC cewa matakin sayar da kungiyar ” yana da wahala gare shi, kuma ”yana jin radadin rabuwa dashi.”
Dama wani biloniya dan kasar Switzerland ya fada wa manema labarai cewa an taya masa kungiyar.
A makon da ya gabata ne Abramovich ya mika ragamar tafiyar da kungiyar hannun gidauniyar amintattun kungiyar biyo bayan kutsawa Ukraine da Rasha ta yi.
Sai dai kuma kawo yanzu Chelsea ba ta mayar da martani kan ikirarin biloniyan ba.
Ana zargin Abramovich mai shekaru 55 da alakar kud-da-kud da Shugaban Rasha Vladimir Putin amma ya musanta hakan.
Tuni Tarayyar Turai ta saka takunkumi ga wasu hamshakan masu arzikin Rasha tare kuma da rike kadarorinsu.
Wannan na zuwa yayin da ake cika mako guda da fara kai hare-hare da Rasha ta yi a Ukraine

