Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam`iyyar APC mai mulki ta fa?a wani sabon ru?ani bayan gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi i?irarin kar?ar jagorancin jam`iyyar a matsayin mu?addashin shugaba na ri?o.
Wasu rahotanni sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sauke shugaban ri?on jam`iyyar, wato Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai mala Buni daga shugabancin jam’iyyar.
Sai dai, wasu ?an kwamitin ri?on jam’iyyar sun musanta hakan. Masana siyasa dai na cewa irin wannan dambarwar shugabanci da APC ke ciki na iya rage ?arfinta a Najeriya.
Duk da cewa an ?auki lokaci mai tsawo ana ta ce-ce-ku-ce kan jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ke yi wa kwamitin ri?on Jam’iyyar APC na ?asa, wani abu da ya ?aure kai, shi ne yadda aka wayi gari a ranar Litinin aka ga Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana a matsayin mu?addashin shugaban jam’iyyar.
Gwamna Sani Bello ya jagoranci manyan jiga-jigan jam’iyyar, kuma ya yi haka ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Shugaba Buhari ya amince da cire Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin ri?on, sakamakon zargin da aka yi cewa ba shi da niyyar gudanar da babban taron jam’iyyar.
Sai dai duk bayan wannan dambarwar, Gwamnan Jihar na Neja Abubakar Sani Bello, ya ce bai san inda maganar ya kar?i shugabanci daga hannun Mai Mala ta fito ba.
A yayin wata hira da manema labarai ya ce abin da ya kawo shi sakatariyar APC shi ne ya je tattaunawa da kwamitin ri?o na APC ya shirya gabannin babban taron jam’iyyar da za a yi.
Haka kuma gwamnan ya ce wani abin da ya kai shi sakatariyar shi ne rantsar da ciyamomi na jam’iyyar inda ya ce bai san tushen zancen da ake cewa ya kar?i kujerar Mai Mala Buni ba.
Ya ce akwai ?a’idoji da ake bi idan ba zai kar?i jagorancin inda ya ce shi ya je ne a matsayin mu?adashin shugaban jam’iyyar domin ci gaba da aikin jam’iyya.
Wannan hawa karagar ri?o ta Gwamna Mai Mala da Gwamna Sani Bello ya yi a matsayin mu?addashi, ya sa mutane da dama suna dasa ayar tambaya a kan lamarin, inda wasu ke cewa da alama salo ne na mamaya.
Haka kuma rashin samun bayanai daga fadar shugaban ?asa kan i?irarin da ake yi na Shugaba Buharin ya amince da sauke shugaban ri?on ko kuma kore batun ya ?ara dagula lamura.
Sai dai a ranar Litinin Jamiyyar APC mai mulki a Najeriyar ta musanta rahotannin da ke cewa an samu sauyin shugabanci a cikinta.
Hakan na ?unshe ne a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai ?auke da sa hannun sakatarenta John James Akpanudoedehe.

