Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa dambarwar da suke yi da ?angaren shugaban ?asar a kan maganar daina amfani da tsofaffin takardun ku?i ta ?ara fito da raunin da shugaban ?asar Muhammadu Buhari yake da shi a fannin jagoranci.
Gwamnan ya sake nanata zargin da yake yi cewa wasu mu?arraban shugaban kasar ne suke ingiza shugaban, yake ?ara turjiya a kan batun canjin ku?in domin su kada jam`iyyar APC a zabe.
A tattaunawarsa da BBC, Gwamna El-Rufai ya ce yana da ya?inin ?an takarar shugaban ?asa na jam`iyyarsu, APC, Bola Tinubu zai ci za?e.
Kuma da zarar ya samu nasara za su fallasa mutanen da ke musu makirci.
Gwamnan ya yi bayani a kan yadda suka cimma matsaya a taron da gwamnonin APC suka yi da shugabannin jam`iyyar cewa ya kamata kowa ya martaba hukuncin kotun ?olin Najeriyar.
Sakamakon taronsu na ?ungiyar gwamnonin APC, gwamnan ya shaida wa BBC cewa, sun tsaya sun duba wannan tsarin da aka ?ullo da shi na canjin ku?i da masifar da abin ya haifar wa al’umma da kuma ?iyayya da ya ce an sa al’umma suka fara ji don su ?ora wa jam’iyyarsu ta APC.

