Site icon Muryar 'Yanci

Rasuwar Idriss Deby Koma Bayace Ga Tsaron Afirka – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Yayin da yake bayyana ka?uwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban gi?i a ?o?arin hadin gwiwa da ake yi na mur?ushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da ka?uwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ?o?arin da yake yi na kare kasarsa.’’

Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a ya?in da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya.

“Sannan ya sanya hannu a yakin da kasar ke yi da Boko Haram, wadanda suka haddasa matsalar tsaro ba a Najeriya ba har da kasashen ta makofta musamman ita kan ta kasar Chadi, da Kamaru da jamhuriyar Nijar,” in ji sanarwar shugaban.

Yayin da yake yi wa al’ummar Chadi da sabon shugaban kasar ta’aziyyar babban rashin da suka yi, Shugaba Buhari ya yi kiran su hada karfi da karfe wajen murkushe masu ta da kayar baya.

Exit mobile version