Site icon Muryar 'Yanci

Rashin Iya Jagoranci Ne Ya Jefa Najeriya Halin Data Ke Ciki – Dr. Umar Ar?o

An bayyana cewar Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama ta fuskar jagoranci na wa?anda ke rike da akalar ?asar, wanda hakan shine babban dalilin da ya jefa ?asar cikin halin ha’ula’i da ta tsinci kanta ciki tsawon lokaci.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani sanannen mai nazari da fashin ba?i akan siyasar Najeriya kuma kwararren masanin tarihi Dr. Umar Ar?o, a yayin tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin tambihi na gidan Talabijin din Liberty dake birnin tarayya Abuja.

Dr. Ar?o ya cigaba da cewar matsalar ?asar ta samo asali ne daga gaza sauke nauyi da wa?anda nauyin kula da harkokin ?asar ke kan kafa?unsu, ?angaren za?a??un da na?a??u da kuma masu e zartar sha’anin mulki, inda kowane guda cikin wannan ?angare ya gaza kai bantenshi abin da ya kaimu ga halin da muke ciki a yanzu.

Masanin tarihin ya kuma ?ora alhakin ?ara ta?ar?arewar al’amurra musanman a yankin Arewa ga wa?anda ya kira masu tsattsauran ra’ayi ta fuskar addini da kabilanci, wanda wannan ba ?aramin illa ya yi wa yankin Arewa ba.

Dangane da yadda harkar tsaro a yankin Arewa ke ?ara fuskantar kalubale da koma baya, Dr.Umar Ar?o ya soki lamirin hukumomin hana fasa ?auri a kasar da Hukumar shige da fice, inda ya bayyana rashin yin katabus din su a ayyukan su sun taimaka wajen jefa kasar cikin mawuyacin hali.
“Babu dalilin da zai sanya muggan makamai su yi yawa a hannun mutane, sannan ba?in haure suna sukuwa a cikin ?asa muddin wadannan hukumomi suna gudanar da ayyukan su yadda ya dace”.

Dr.Ar?o ya kuma soki lamirin Sojoji bisa ga kutsen da suka yi akan sha’anin mulki a kasar, wanda wannan ya yi wa kasar illa da mayar da ita ajin baya, a tsakanin sauran ?asashen duniya.

Akan batun da ake ta magana na yin sulhu ko kuma ?aukar matakin bu?e wuta ga ‘yan Bindiga kuwa, masanin tarihin ya bayyana cewar harkar tsaro takan fara ne tun daga matakin gundumomi har zuwa jiha sannan tarayya, sannan a halin da tsarin Najeriya ke ciki yanzu Gwamnoni ba su da wani ?arfi akan sarrafa jami’an tsaron dake Jihohin su sai dai su nemi alfarma, to tun da lamarin a harkar yake gyara zai yi wuya.

Exit mobile version