Site icon Muryar 'Yanci

Rashin Adalcin Da ‘Yan Najeriya Ke Yi Wa Buhari Ya Wuce Hankali – Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya roki yan Najeriya su daina ?ora wa shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, laifin duk kalubalen da suke fuskanta a ?asa.

Amaechi, wanda tsohon shugaban ?ungiyar gwamnoni ne, ya yi wannan furucin yayin wata hira da Channels TV mai taken, “Hard Copy.”

Minsitan ya yi ikirarin cewa mutane suna zargin shugaban ?asa Buhari da abin da bai shafe shi ba, inda suke ?ora wa shugaban laifi akan abin da hakki akai.

“Komai muka ?auko sai mu dora wa gwamnati, yadda kasan nan gaba idan mutane ba su samu juna biyu ba, za su ce laifin Buhari ne.” Ministan ya ?ara da cewa shugaba Buhari ya samu ?asar nan ba yadda yake tsammaninta ba, kuma yana iyakacin bakin kokarinsa.

Da aka tambaye shi ko mai yasa Buhari ya gaza saita komai a Najeriya kamar yadda ya yi al?awari ga shi har ya shafe kusan shekara 7, Amaechi yace ba komai ne za’a samu yadda ake so ba. Buhari ne ya farfa?o da tattalin arziki, A cewar ministan gwamnatin shugaban kasa Buhari ta bullo da hanyoyin samun kudin shiga a gwamnatance, ba ta dogara da hanya ?aya ba.

Amaechi ya kara da cewa wannan gwamnatin ta farfa?o da tattalin arzikin ?asa kuma ta dakatar da shigo da shinkafar kasashen waje ta bunkasa fannin noma.

Dangane da batun lalacewar tsaro a kasa kuwa, ministan yace matsalar tsaro da ta ?i ci ta ?i cinyewa a Najeriya, ba zai yuwu a magance ta ba har sai gwamnati ta kawar da talauci a karon farko.

Exit mobile version