Site icon Muryar 'Yanci

Rashin Adalci Ne Takarar Musulmi Da Musulmi A Najeriya – Atiku

?an takarar shugaban ?asa a ?ar?ashin PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba daidai ba ne da jam’iyyar APC ta tsayar da ‘yan takarar shugaban ?asa da mataimakin sa duk Musulmai a za?en 2023.

Ya ce ya yi mamakin da APC za ta za?i wannan baibawan-burmin siyasa, a ?asa kamar Najeriya mai mabiya addinai da al’adu ba ?aya ba.

Haka Wazirin Adamawa ya bayyana a tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise TV ta yi shi a ranar Juma’a.

A ranar 10 Ga Yuli ne Bola Tinubu ya bayyana sunan tsohon Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar sa.

TInubu da Shettima duk Musulmai ne, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya.

Atiku ya ce batun tikikin Muslim-Muslim shi ne kusan kandagarkin da ya yi masa katanga da Tinubu, shekaru da da?ewa tun ma kafin kafa APC.

Atiku ya bayyana yadda ya ?i goyon bayan a yi tikitin ‘Muslim-Muslim’, lokacin da za?en 20215 ya zo.

“Ni ban yarda a ce daidai ne a ?asa kamar Najeriya mai ?abilu da addinai mabambanta, amma a ce wai a fitar da ?an takarar shugaban ?asa da ?an takarar mataimakin shugaban ?asa duk Musulmai.” Inji Atiku.

Atiku ya ce duk da cewa ?an takarar mataimakin shugaban ?asa na APC wato Shettima a yankin Arewa maso Gabas ya ke, inda Atiku ya fito, duk da haka Atiku ya ce shi ne ya fi alamun yin nasara a za?en shugaban ?asa da za a yi cikin 2023.

Duk da Atiku ya ce Tinubu abokin sa ne, ya ?ara da cewa hakan bai hana ra’ayin su ya bambanta a fagen siyasa.

Exit mobile version