Site icon Muryar 'Yanci

Rashin Adalci Da Son Zuciya Ya Sa Ake Sukar Gwamnatinmu – Buhari

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka akan masu sukar Gwamnatinshi ba tare da wata ?a??waran hujja ba, inda ya ce mulkinsa yayi rawar gani tun bayan da ya hau karagar Shugabanci a 2015.

Shugaban Kasar ya sanar da hakan ne a tattaunawa ta musamman da yayi da gidan talabijin na kasa (NTA) a ranar Juma’a.

Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su dinga yi wa mulkinsa adalci idan suka tashi yanke hukunci ya zamana idan an ciza sai a hura sannana ya kara da cewa jama’a su dinga duba abinda ya samar a mulkinsa da kuma abinda akwai kafin ya hau karagar jagorancin Najeriya.

“Ina son ‘yan Najeriya su dinga yi wa mulkin nan adalci. Su kasance masu tuna baya lokacin da ba mu iso ba, ballantana a abubuwan da suka shafi arewa maso gabas da kudu maso kudancin kasar nan,”. “Zan so ‘yan Najeriya su dinga tuna wadannan abubuwan lokaci zuwa lokaci kuma ina da tabbacin bamu yi mugun abu ba.”

Exit mobile version