Wannan Rana ta 8 ga watan Maris Ita ce ranar ?ancin Mata ta Duniya wacce majalijsar ?inkin Duniya ta ware domin a jaddada muhimmanci da kuma matsayi da Mata suke da shi a jagoranci.
Dan haka ma yasa aka yi wa wannan rana ta bana taken ‘Mata A Jagoranci’ saboda ?imbin mahimmancin da suke da shi a rayuwar mu ta yau da kullum.
Shugaban ?ungiyar Kare ha??in Bil’adama Da Taimakawa masara ?arfi ta rigar yanci International Foundation For The Less Privileged, Mustapha Haruna Khalifa ne ya fa?i haka a lokacin zantawa da manema labarai a kaduna.
Ya ce wannan shekara ta 2021 ta zo mana da wani yanayi idan aka yi Duba da yadda ake tauye ha??in Mata a ?angarori daban-daban na zamanta kewa musamman Fya?e.
Domin a bana kawai daga ranar 1 ga watan Janairun 2021 zuwa yau 8 ga watan Maris matsalolin cin zarafin ?a?a mata da suka zo gaban mu suna da yawan gaske ciki har da Mahaifin da yayi wa ?iyar cikin sa fya?e, Inji shi.
Da kuma Mahaifin da ya ce kada ?a?an sa Mata su sake amsa sunan sa a ko’ina kuma in ya mutu basu da gadon sa wannan rashin tausayi da ?in kimanta Mata yana daga cikin abubuwan da ba zai yiwu mu mance Da shi kuma mu zura musu Ido ba.
Dan haka ya zama Dole mu tashi mu ya?i cin zarafin ?a?a Mata a lunguna da sa?o na duk inda muka samu kan mu wannan zai sa mu zama jakadu na kare ha??in Bil’adama a fa?in Duniya.
A ?arshe muna kira ga Hukumomin tsaro da na Shari’a da su ba mu Ha?in kan da ya kamata wajen hukumta duk wani wanda aka samu da cin zarafin ?a?a Mata ta kowacce Hanya.
Sa Hannu:
Ameera Abdul?adeer,
Communication & Information,
Rigar Yanci International.

