Rahotanni daga birnin Yola na Jihar Adamawa na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban ?asa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana ya?ininsa cewa yan Najeriya zasu sake mi?a ragamar mulkin Najeriya ga jam’iyyar PDP a 2023.
Atiku ya ro?i yan siyasa su girmama dokokin za?en jam’iyya da kuma kundin tsarin mulkin ?asa yayin gudanar da kowane irin za?e.
Tsohon mataimakin shugaban yana cewa matu?ar ana son ?orewar demokara?iyya to sai an tabbatar da ingancin za?e. Yan Najeriya basu da wani za?i da ya wuce jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi jim ka?an bayan ya ka?a kuri’arsa a wurin taron za?en shugabannin PDP a matakin jiha a mazabarshi dake Jihar Adamawa.
“Idan kuka duba zaku ga yadda zaben ke tafiya cikin adalci kuma ba ?oye-?oye a lokuta da dama muna zama ne mu amincewa juna a kowane mataki.”
Rahoto ya nuna cewa sama da wakilan PDP 2,614 daga ?ananan hukumomi 21 na jihar Adamawa ne suka ka?a kuri’arsu a wurin za?en.
Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, shima ya samu damar zuwa ya ka?a kuri’arsa a wurin babban taron jam’iyyarsa ta PDP.

