Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lami?o ya ?aryata rahoton da ya ce Dattawan Arewa da yan takarar PDP na shugabancin ?asa sun za?i tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a matsayin yan takarar da Arewa za ta tura wakilci a za?en fidda-gwanin PDP.
Jaridar Vanguard ce dai ta buga labarin cewa Dattawan Arewa sun tsayar da Saraki da Bala Mohammed yan takarar su na za?en fidda-gwani wanda za a yi a ranar 28 Ga Mayu, 2022.
Jaridar ta ce wannan matsaya da suka ?auka na ?unshe cikin wata takardar bayan taro da dattijo Ango Abdullahi ya sa wa hannu, cewar Vanguard.
Sanarwar ta ce Dattawan Arewa ?in sun za?i yan takarar biyu daga cikin hu?un da suka mi?a sunayen su domin tantancewa.
Lami?o ya ce maganar gaskiya ba a ta?a zama an cimma wannan yarjejeniyar ba. Ya ce wannan dai raayi ne kawai na wasu dattawan da suka fitar da sanarwar kawai.
Shugabannin PDP masu ruwa da tsakin ta na Arewa ba su san da wannan magana wadda rahoton ta buga ba. Maganar wai wasu Dattawan Arewa sun za?i yan takara biyu daga cikin dukkan yan takarar Arewa da suka cancanta a PDP, don su tsaya za?en fidda gwani ba gaskiya ba ce.

