Fadar Shugaban ?asa ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban ?asa Olusegun Obasanjo ya yi a sa?onsa na sabuwar shekara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai ta?a daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina ba?in ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ?asa ba.
Fadar shugaban ?asar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana al?awura a kanta.
Haka kuma fadar shugaban ?asar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ?arya domin ya samu ?uri’unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ?uri’unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.
Fadar shugaban ?asar ta kuma ce Obasanjo yana ba?in ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da’awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin za?e fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.

