Site icon Muryar 'Yanci

NNPC Ta Zargi Masallatai Da Majami’u Da Satar Danyen Mai

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin Man Fetur na ?asa NNPC ya zargi jami’an gwamnati, malaman addini, hukumomin tsaro da ma wasu ma’aikatanta da hannu wurin satar danyen mai a kasar.

Da ya ke magana a wurin taron tawagar shugaban kasa karo na 49 a gidan gwamnati a Abuja, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce dukkan rukunin mutanen kasar na da hannu a laifin.

Ya bayyana cewa duk lokacin da aka samu kayan satar a masallatai da coci-coci, akwai wasu masu barnata kayan gwamnati da ke aiki da su. Kyari ya ce: “A lokacin da aka samu gobara daya cikin bututun mu, mun gano bututun ta shiga gidajen wasu mutane. Bayan haka, duk da nuna cewa mu masu addini ne, ka san cewa wasu daga cikin bututun da danyen man mun gano su a coci-coci ne da masallatai.

“Hakan na nufin kowa na aikata laifin. Babu yadda za a yi ka kwaso kaya ka loda a motoci zuwa unguwanni da akwai mutane da dama ba tare da wani ya ganka ba. Kowa har da mutanen unguwa, malaman addini da kuma wata kila jami’an gwamnati, ciki har da jami’an tsaro suna ciki.

Exit mobile version