Rahoton dake shigo mana daga Jihar Ebonyi na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada matsayarsa cewa kotu ce ka?ai za ta tantance matsayin jagoran ‘yan ?ungiyar aware masu neman kafa ?asar Biafra, Nnamdi Kanu.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ganawarsa da shugabannin ?abilar Igbo a Jihar Ebonyi bayan jagororin sun ro?e shi ya saki Kanu, wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a a gaban kotu kan zargin tayar da hankali da raba kan ‘yan ?asa.
“Na saurari ro?on dattijai da shugabannin gargajiya daban-daban da kyau game da batutuwa,” in ji Buhari. “Kuma kamar yadda na fa?a a baya, wannan lamarin zai ci gaba da kasancewa a hannun kotu, inda za a ba shi kulawar da ta dace.”
Ya ?ara da cewa: “Damuwata ita ce fararen hularmu wa?anda da ma can rayuwarsu na cikin ?unci kuma suke so su fita kawai don su nemi abin da za su ci abinci.”

