Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain sun ce mutumin ya yi yun?urin halaka Sheikh Bandar Baleelah ne lokacin da yake gabatar da hu?ubar Sallar Juma’a.
Haramain Sharifain ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata 25 ga watan Mayu cewa, mutumin wanda ?an ?asar Saudiyyan ne mai shekara 40, ya yi ikirarin cewa shi Imamu Mahdi ne.
Ya fa?i hakan ne a yayin da ?an sanda suke tuhumarsa. Sai dai hukumar ba ta yi ?arin bayani kan matakin da aka ?auka a kansa ba.
Mutumin ya yi ?o?arin aikata wannan aika-aikar ne a yayin da yake sanye da harami a jikinsa.
Imamu Mahadi shi ne wani mutum da wasu Musulmai suka yi imanin cewa zai zo a ?arshen duniya.
Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafukansa na sada zumunsa yadda mutumin ya yi yun?urin kutsawa ga limamin da kuma yadda jami’an tsaro suka mur?ushe shi.
Hukumomin sun ce “mutumin ya tunkari mumbarin limamin ne ri?e da makami a masallacin Ka’aba amma an yi nasarar mur?ushe shi.”

