Site icon Muryar 'Yanci

Ni Da Siyasa Mutu Ka Raba – Shekarau

Sanata Ibrahim Shekarau ya ce ba zai yi murabus daga siyasa ba har sai ya mutu, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan rantsar da majalisar Shura ta jihar Kano, Shekarau ya ce “ba ni da lokacin yin murabus daga siyasa har sai na mutu.”

Tsohon gwamnan har sau biyu na jihar Kano, ya samu mukamin ministan ilimi daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma yayi fafutuka a zaben 2015 ba kadan ba.

“A takaice, abinda yasa na zo ina magana shine in musanta lamarin. A wurina gaskiya babu ranar murabus daga siyasa.

“Ina fadin wannan kusan shekaru 20 da suka gabata. Siyasata ita ce addinina, addinina shine siyasata kuma babu lokacin da zan bar addinina saboda dukkan biyun suna aiki tare ne.

“Addini shine bautawa Ubangiji kuma kololuwar bautawa Ubangiji shine bautawa jama’a da suka kasance halittar Ubangiji. Kamar yadda na sani Musulunci ya koyar da cewa duk wani taimako da ka baiwa wani, kana cika umarnin Ubangiji ne. Idan na yi maka addu’a ko kyautatawa, nau’in ibada ne.

“Idan na kai shekaru 90 na tsufa ba zan iya takara ko fita gangamin siyasa ba, zan iya bada shawara ga jama’a ina daga kwance. Siyasa hanya ce ta bautawa jama’a, hakan na dauka.

“A don haka ne yasa nake tausayin duk wanda yace zai yi murabus daga siyasa. Ta yuwu bai gane mene ne siyasa ba. Sun tsayar da ita a samun mukami, fita takarar gwamna, sanata ko wani mukami.

“A fahimta ta, siyasa ita ce kwarewar mutum wurin mu’amala da jama’a tare da bautawa jama’a ta duk hanyar da ta kama. Don haka bani da ranar murabus daga siyasa. Ina nan har sai na mutu.”

Exit mobile version