Dakatacciyar shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya, Hadiza Bala ta bayyana cewa, ita da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, takalmin kaza ne, Ogan ta ne na dindindin babu tantama akai.
Hadiza ta rubuta a shafinta ta Facebook a karkashin wani hotunta zaune da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a Zariya wajen hawan karamin Sallah a fadar mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli.
Eid Mubarak .Taqabbalall?hu minn? wa minkum.
Allah ya amsa ayyukan mu na kwarai. Ina fadar mai martaba sarkin Zazzau tare da shugabana na har abada @El-Rufai. Muna nan daram dam, domin akan gaskiya muka dogara a koda yaushe. Muna rokon Allah ya kare mu yayi mana jagora, Amin.
Idan ba a manta ba, kafin a nada Hadiza shugabar Hukumar NPA, ita ce shugabar maaikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna.

