Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa Manyan jiga-jigan jamiyyar PDP sun kaiwa tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ziyarar bangirma a gidansa.
Shugaban jamiyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan tsohon shugaban kasar da ke unguwar Hilltop a garin Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Talata.
An gano tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye a cikin tawagar, sauran wadanda ke a tafiyar sun hada da mataimakin shugaban PDP na kasa a arewa, Cif Tom Ikimi, tsohon gwamna Nwodo, sakataren labaran jamiyyar na kasa da kuma shugabar matan jamiyyar na kasa.

