Site icon Muryar 'Yanci

Neja: Zaratan Mafarauta Sun Hallaka Gaggan ‘Yan Bindiga 47

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar wasu Zaratan Mafarautar Gargajiya sun yi nasarar kashe ‘Yan bindiga 47 da suka hana mutanen Shiroro dake Jihar Niger zaman lafiya na dogon lokaci.

Rahotanni sun bayyana cewar mafarautar sun kaddamar da harin ne a Magami dake tsakanin kananan hukumomin Shiroro da Rafi inda suka hallaka ‘Yan bindigar a ranar larabar da ta gabata.

Majiyarmu tace ‘Yan bindigar sun dade suna amfani da yankin dake kusa da gabar ruwa wajen fakewa suna kaiwa jama’a hare hare a yankunan jihar.

An ruwaito wani jami’in ‘Yan sanda ya tabbatar da cewar bayan kashe 47 daga cikin su, wasu da dama sun tsere da harbin bindiga a jikin su.

Jihar Niger na daya daga cikin jihohin da ‘Yan bindiga suka hana jama’a sakewa, inda suke kai hari garuruwa suna kashe mutane da kuma kwashe wasu domin karbar kudin fansa.

Exit mobile version