Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar ‘Yan bindigar da suka tsare kwamishinan harkokin yada labarai na jihar, sun tuntubi yanuwansa, sun bukaci a biya kudin fansa na miliyoyin kudade.
An ruwaito cewa yan bindigan da su ka yi garkuwa da Malam Sani Mohammed Idris, sun fada wa iyalinsa su kawo Naira miliyan 500. Rahoton da aka fitar a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021, ya ce miyagun yan bindigan sun ce sai an biya kudin sannan kwamishinan zai fito.
An yi garkuwa da Sani Mohammed Idris a jiya kamar yadda rahotanni suka bayyana, an dauke mai girma Kwamishinan ne a kauyensa cikin dare a karamar hukumar Tafa, a jihar Neja.
Kwamishinan yada labaran ya na yawan kai ziyara zuwa gida domin duba ganin aikin da ake yi a gonakinsa, sannan kuma ya gana da yanuwansa.
Dauke kwamishinan ya sa mataimakin gwamna, Ahmed Muhammad Ketso ya jagoranci taron harkar tsaro na musamman da aka shirya. Bisa dukkan alamu, gwamna ba ya jihar, don haka mataimakin gwamnan jihar Neja, Alhaji Ahmed Muhammad Ketso ya kira zaman gaggawa.
Har zuwa yanzu babu labari daga jamian tsaro da hukumomi cewa an ceto wannan Bawan Allah, kuma yanuwansa ba su bayyana halin da ake ciki ba.

